Ana zaben shugaban kasa a Algeria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ba sakafai shugaban ke bayyana a bainar jama'a ba

Ana zaben shugaban kasa a kasar Algeria, inda shugaban kasa mai ci, Abdul Aziz, Boteflika ke neman wa'adin mulki na hudu.

Shugaban kasar wanda ya samu cutar bugun jini a bara, ya kada kuri'arsa ne yana kan keken guragu.

Hadakar jam'iyyun masu kishin Islama da wadanda ke da ra'ayin raba siyasa da addini sun bukaci a kaurace wa zaben.

Suna zargin cewa zaben ba na gaskiya ba ne, domin shugaban ba shi da koshin lafiyar da zai yi mulki.