Soji sun janye cewa an ceto 'yan mata da dama

Image caption Abubakar Shekau ya sha alwashin kashe masu adawa da Boko Haram

Sojin Najeriya sun janye sanarwar da suka yi jiya cewa an ceto galibin 'yan makarantar da 'yan bindiga suka sace a Chibok.

Janye kalaman na sojin ya biyo bayan musanta zancen sojin ne Shugabar makarantar da kuma gwamnatin jihar Borno.

A jiyan rundunar tsaron Nigeria ta yi ikirari ne cewa an kubutar da 'yan matan sauran takwas ne kawai daga cikin 129 da wadanda ake zaton 'yan Boko Haram ne suka sace.

Sai dai wakilin BBC a Abuja ya ce, babu wata majiya mai zaman kan ta da ta tabbatar da wannan kuma wasu 'yan sa'o'i gabanin wadannan bayanan, gwamnan jihar Borno ya fada cewar har yanzu ba a ga 'yan matan da dama ba.

Wasu daga cikin iyayen da aka zanta dasu sun ce har yanzu ba suga 'ya'yansu ba.

Wannan rashin tabbas da game da wadannan 'yan matan, kamar yadda masu sharhi suka bayyana wata alama ce dake nuna cewar akwai jan aiki a gaban hukumomin Nigeria a yinkurinsu na murkushe ayyukan 'yan Boko Haram.

Ana hasashen cewar 'yan Boko Haram sun tafi da matan cikin dazukan da ke kusa da kan iyakar kasar da Jamhuriyar Kamaru.

A cikin wannan shekarar 'yan Boko Haram sun yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 1,800 a Nigeria.

Karin bayani