Shugabar makaranta ta musanta maganar sojoji

Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sai nan gaba ne ake fatan tantance yawan daliban da ba a gani ba

Shugabar makarantar 'yan matan nan da aka sace a garin Chibok, Asabe Kwambura ta musanta gaya wa rundunar sojin Nigeria cewa 'yan mata takwas ne suka rage ba a gani ba.

Malama Asabe ta kara da cewa ba gaskiya ba ne cewa, an kubutar da 'yan matan fiye da 100.

A wata hira da BBC, Asabe ta ce an bude rajista a makarantar inda aka bukaci iyayen yara su je su rubuta sunayen 'ya'yansu da har yanzu ba a gani ba.

A ranar Laraba ne kakakin rundunar sojin kasar, Manjo janar Chris Olukolade a wata sanarwa ya ce shugabar makarantar ta tabbatar musu da cewa 'yan mata takwas ne suka rage ba a gani ba.

Shugabar ta yi karin haske cewa lokacin da aka sace 'yan matan, babu sojoji sai masu gadin makarantar, ko da yake da rana akwai 'yan sanda hudu dake zama a makarantar har sai yara sun kammala rubuta jarrabawa.