An tsayar da ranar shari'ar Karim Wade

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu jama'a sun yi zanga-zanga domin neman a sake shi a watan Oktobar 2013

Jami'an gwamnatin Senegal sun ce an tsayar da watan Yuni, domin yin shari'ar Karim Wade dan tsohon shugaban kasar bisa zargin cin hanci da rashawa.

Ana zarginsa da azurta kansa da fiye da dalar Amurka biliyan daya, a shekaru 12 da mahaifinsa Abdullahi Wade ya yi a kan mulki.

Karim ya mallaki kadarori da suka hada da gidaje, motocin kasaita da kamfanonin hada-hadar kudade na kasashen waje.

Shekara guda kenan da ake tsare da Karim a kurkukun Dakar, ko da yake ya musanta zarge-zargen da ake masa.