Najeriya- Taron gaggawa da majalisar tsaro

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan zai gudanar da taron gaggawa da Majalisar tsaron kasar kan tabarbarewar al'amuran tsaro a kasar.

Wata sanarwa da ta fito daga mai baiwa shugaban kasar shawara ta fuskar yada labarai Reuben Abati ta ce shugaban kasar ya kuma gayyaci wasu gwamnoni da zai tattauna da su kan sha'anin tsaro bayan ya kammala ganawa da Majalisar tsaron kasar.

Sanarwar da mai baiwa shugaban Najeriya shawara ta fuskar yada labarai ya aikewa BBC, ta ce daga cikin wadanda zasu halarci taron sun hada da mataimakin shugaban kasar, ministan tsaron kasar, da sauran manyan hafsoshin tsaron kasar da babban sipeton 'yansandan Najeriyar.

Sanarwar dai ta kara da cewa shugaba Jonathan da Majalisar tsaron kasar dama gwamnonin kasar za su yi nazari kan al'amuran tsaro, da kuma irin matakan da ake dauka yanzu da nufin lalubo hanyar magance matsalar.

Shugaban kasar dai a sanarwar ya bayyana takaicin sa kan dalibai matan da aka yi awon gaba da su a wata makarantar sakandare dake jihar Borno.