Ba zan tura sojoji zuwa Ukraine ba - Putin

Hakkin mallakar hoto RIA Novosti
Image caption Shugaba Vladmir Putin

Shugaba Putin ya ce yana fatan ba zai zame ma sa dole ba ya yi amfani da abun da ya kira 'yancinsa na tura sojoji zuwa Ukraine.

A wata hira ta waya da ya saba yi kowacce shekara, Mr Putin ya musanta cewa Rasha tana da hannu a a tarzomar da ake yi a gabashin kasar ta Ukraine, amma a karon farko ya amsa cewa sojojin Rasha sun shiga yankin Crimea.

Shugaba Putin ya kara da cewa ta hanyar tuntuba ce kawai zaa iya warware rikicin na Ukraine, yana mai cewa tattaunawar da ake yi a Geneva tana da muhimmancin gaske.

Hakazalika Mr Putin ya amsa tambaya daga tsohon jami'in leken asirin na Amurka, Edward Snowden, wanda ke gudun hijira a Rasha.

Mr Putin ya fada masa cewa Rasha ba ta yarda a rika sauraren magangangun 'yan kasarta ta waya ba ko kuma tare sakonninsu na salula.

Karin bayani