Ana ci gaba da aikin ceto a Korea ta Kudu

Aikin ceton pasinjojin jirgin ruwan Korea ta Kudu Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Aikin ceton pasinjojin jirgin ruwan Korea ta Kudu

An shiga rana ta biyu na ayyukan ceton mutane 300 da suka bata, bayan da jirgin ruwan daukar pasinja ya nutse a ruwan Korea ta Kudu.

Yanzu haka masu kai agajin gaggawa sun maida hankulansu kan tarkacen jirgin, wanda ya nutse a cikin ruwan.

Mai magana da yawun jami'an 'yansanda masu gadin gabar tekun Korea ta Kudun ya ce rashin kyaun yanayi a karkashin ruwan na kawo cikas wajen kokarin da ake na aikin ceton.

Masu kai agajin dai sun shafe daren jiya ne suna laluben lungu da sakon tarkacen jirgin da ya nutse a cikin ruwan Korea ta Kudun ta hanyar amfani da manyan fitilu.

Pasinjoji kusan dari uku ne dai suka yi batan dabo bayan da hatsarin ya abku, kuma akasarinsu yara ne 'yan makaranta.

Kawo yanzu an ceto mutane fiye da dari da saba'in daga cikin jirgin ruwan, wanda ya nutse a wani yanki mai zurfin mita talatin.

Hukumomin dai na cewa babu alamun yiwuwar sake samun sauran pasinjojin da rai.