An cin ma 'yarjejeniyar zaman lafiya a Yukuren

John Kerry da Sergei Lavrov Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption John Kerry da Sergei Lavrov

An cin ma 'yarjejeniya don rage zaman zullumi a Ukraine a tattaunawar da ake yi a Geneva.

Masu shiga tsakani na Amurka da Tarayyar Turai da Yukuren da kuma Rasha sun amince cewa ya kamata a rusa duka kungiyoyin sa-kai da aka kafa ba bisa ka'iba ba a Ukraine.

Za su kuma ajiye makamansu, su kuma fice daga harabobi da kuma gine-ginen gwamnatin da suka mamaye.

Ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov, Sergei Lavrov yana cewa ya kamata a yi wa masu zanga-zangar ahuwa, in banda wadanda suka aikata miyagun laifufuka.

Shi kuwa Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, yabawa ya yi da sakamakon tattaunawar, amma ya ce ba shi da wani zabi, illa ya sakawa Rasha karin takunkumi, idan har ta nuna cewa ba da gaske take ba wajen rage zullumin da ake ciki a kasar ta Yukuren.

A kafin sannan kuma a yau din, a wata hira ta waya da ya saba yi kowace shekara, Shugaba Putin Rasha ya musanta cewa Rasha tana da hannu a a tarzomar da ake yi a Gabashin kasar ta Yukuren.

Shugaba Putin na Rasha ya ce, yana fatan ba zai zame masa dole ba ya yi amfani da abun da ya kira 'yan cinsa na tura sojoji zuwa Ukraine.

Amma a karon farko ya amsa cewa, sojojin Rasha sun shiga yankin Crimea.

Shugaba Putin ya kara da cewa ta hanyar tuntuba ce kawai za a iya warware rikicin na Ukraine.