Buhari ya yi barazanar kai PDP kotu

Image caption Janar Muhammadu Buhari

Tsohon Shugaban Nigeria Janar Muhammadu Buhari ya yi barazanar kai jam'iyyar PDP gaban kuliya kan danganta shi da kungiyar Boko Haram.

Jigon na Jam'iyyar adawa ta APC a cikin watan sanarwa ya nuna damuwa a kan abinda ya kira kokarin bata masa suna daga bangaren jam'iyyar PDP, inda ya baiwa jam'iyyar kwanaki 7 da ta janye waccan maganar ko kuma ya nufi kotu.

Janar Buhari ya kuma bukaci PDP ta nemi afuwarsa a bainar jama'a saboda kokarin alakantashi da tashe-tashen hankulan da ake fama da su a kasar.

Kakakin Jam'iyyar PDP Olisah Metuh ne ya fitar da wata sanarwar da Janar Buhari ya ke neman afuwa a kai.

A cewarsa "Ba zan zauna ba, in bari a bata min suna dana jam'iyyata ba duk da sunan siyasa".

Janar Buhari ya ce kungiyar Boko Haram ta 'yan ta'adda ce tun kafin zabukan shugaban kasa na shekara ta 2011 ta ke gudanar da ayyukanta.

Karin bayani