An kai ma 'yan gudun hijira hari a Sudan

Sojojin sa kai a Sudan ta Kudu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin sa kai a Sudan ta Kudu

Babban jami'in hukumar ba da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu Toby Lanzer ya gaya ma BBC cewar an kashe farar hula da dama a wani hari da aka kai kan wani sansanin Majalisar Dinkin Duniyar dake Bor babban birnin jihar Jonglei.

Mr Lanzer yace wasu matasa ne kimanin dari ukku suka tinkari sansanin da hantsi suna kokarin gabatar da wani koke. Daga nan suka balle kofofin shiga cikin sansanin suka fara bude wuta kan mai tsautsayi.

Dakarun kiyaye zaman lafiyar sun harba bindigogi na gargadi, amma suka cigaba da bude wutar ba kakkautawa, lamarin da ya sanya su mayar wa maharan martani.

An dai raunata dakarun biyu. Farar hular kimanin dubu biyar ne suka nemi mafaka a sansanin dake garin da yaki ya daidaita.

Karin bayani