Sabon salo game da rikicin Rasha

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ukraine ta shiga cikin rudu

Masu zanga-zangar nuna goyon bayan Rasha a gabashin kasar Ukraine sun kara wasu jerin sharudda ga yarjejeniyar da aka cinma da kasashen duniya na cewa su fice daga dukkan gine-ginen da suke mamaye da su, su kuma ajiye makamansu.

Shugabannin masu zanga-zangar a birnin Donetsk sun ce sai gwamnatin rikon kwaryar da shugaban rikon dake Kiev sun fara sauka tukuna, domin sun karbi iko ne da ta hanyar juyin mulki.

Firaministan Ukraine na riko, Arseniy Yatsenyuk, ya kara jaddada kiran nasu " Ina son in bayyana cewa tuni gwamnatin Ukraine ta shirya doka ta yin afuwa".

Masu zanga-zangar a Donetsk suna ta kara karfafa shingayen da suka kafa da tayoyi da kuma katako, yayinda su ma sauran masu zanga-zangar a sauran birane takwas na gabashin kasar ke ci gaba da mamaye wuraren.

Karin bayani