An cimma yarjejeniya kan rikicin Ukraine

Tattaunawa kan kasar Ukraine Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tattaunawa kan kasar Ukraine

An cimma yarjejeniya kan warware rikicin dake gudana a kasar Ukraine, a wata ganawa da aka yi tsakanin wakilan kasashe da dama a Geneva.

Ministocin harkokin wajen kasashen Rasha da Ukraine da Tarayyar Turai da Amurka sun amince cewar kungiyoyin masu gwagwarmaya su ajiye makaman su, su kuma fice daga gine-ginen gwamnati da suka mamaye a fadin kasar Ukraine.

A wata sanarwa ta hadin-gwiwa, Ministocin sun ce za a yi afuwa ga 'yan gwagwarmayar da suka yi aiki da umurnin muddin dai ba a same su da laifin tafka miyagun laifukka ba.

Ministan harkokin wajen Ukraine Andriy Deshchytsia ya ce kasarsa za ta yi tsayin daka kan yarejejeniyar duk da cewa bai amince da kasar Rasha ba kan dalilan da suka haddasa rikicin.

Sai dai kungiyoyi masu fafitikar goyon bayan kasar Rashar a birnin Donestsk ba su nuna wasu alamun ficewa daga gine-ginen da suka mamye ba.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya ce ganawar da suka yi jiya ta yi armashi, amma Shugaba Obama ya nuna tababa kan ko Rasha za ta mutunta bangaren ta na yarjejeniyar.