'Yan mata 14 sun sake kubuta a Borno

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan mata 14 sun sake tserewa daga hannun 'Yan Boko Haram

Kwamishinan ilimi a Jihar Bornon Najeriya ya ce akalla 'yan mata goma sha hudu ne suka sake tserewa daga hannun masu tada kayar baya da suka sace su tun a daren Litinin din da ta gabata.

Musa Inuwa Kubo ya ce a yanzu haka 'yan mata arba'in da hudu ne sukai nasarar gudowa daga hannun maharan da suka kame su, sai dai har yanzu ba a ga wasu tamanin da biyar ba ya yin da iyayen yaran ke cewa wasu da dama ba a gansu ba.

Jami'an tsaro da 'yan kato da gora da ma iyalan 'yan matan na ci gaba da nemansu, wadanda ake kyautata zaton 'ya'yan kungiyar Jama'atu AhlusSunna Lidda'awati wal Jihada da aka fi sani da Boko Haram ne suka sace 'yan matan.

Wakilin BBC yace a baya 'ya'yan kungiyar Boko Haram sun sha sace 'yan mata a kasar, sai dai yawansu bai kai na wannan karon ba.

Karin bayani