Chibok: Dalibai 45 sun kubuta

Gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gwamnan Jihar Borno Kashim Shettima

Wasu karin 'yan mata daga cikin wadanda ake zargin 'yan Boko Haram sun sace su a makarantar mata ta Chibok a Jihar Borno sun kubuta.

Kwamishinan Ilimi na Jihar Bornon Musa Inuwa Kubo ya shaidawa BBC cewa kawo wa yanzu 'yan mata 45 su ka kubuta, yayinda har yanzu ake neman sauran 84.

Kwamishinan ya kuma ce zasuyi 'duk abunda ya kamata' don ganin cewa sun kubutar da daliban.

A makon jiya ne wasu 'yan bindiga suka sace daliban daga wata makarantar sakandiren mata a garin na Chibok.

Karin bayani