Rasha da Ukrain na zaman doya da manja

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ukarin da Rasha na zaman doya da manja

Yarjejeniyar da aka cimma a Geneva a ranar Alhamis dan rage zaman tankiya a kasar Ukraine na fuskantar baraza, sakataren harkokin wajen Amurka john Kerry ya magana ta wayar tarho da manyan jami'an gwamnatin Rasha da Ukraine.

Wani jami'in ma'aikatar harkokin wajen Amurka ya ce Mr Kerry ya bukaci Rasha da ta aiwatar da cikakkiyar yarjejeniyar da aka amince da ita.

Tun da fari shugaban riko na Ukraine Oleksandr Turchynov ya ce za a kyale jami'an kananan humumonin Ukraine su yi amfani da yaren kasar Rasha.

Ya kuma ce domin samun zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin 'yan Ukraine, za a kyale shugabannin yankuna da birane da gundumomi su rika amfani da yaren kasar Rasha ko kuma wani yare da mafi yawan al'umar yankin ke amfani da shi.

A bangare daya kuma Mr Kerry ya bawa gwamnatin Ukraine ya yi kan matakan da ta ri ga ta dauka na aiwatar da yarjejeniyar.

A jiya juma'a ne dai magoya bayan Rasha suka ki amincewa da barin gine-ginen gwamnati da suka mamaye a gabashin Ukraine, inda suka dage kan cewa sai shugaban Kiev ya sauka daga mukaminsa.

Karin bayani