An kai hare-hare a Jihar Bauchi

Hakkin mallakar hoto bbc

Wasu 'yan bindiga sun kai hare-hare a Jihar Bauchi dake arewa-maso-gabashin Najeriya, inda su ka kone barikin 'yan sanda da gine-gine da dama.

Maharan sun kuma kone na'urorin kamfanin salula na Glo da motoci fiye da 20 da kuma wata makaranta.

Hare-haren wadanda aka kai a garin Yana dake karamar hukumar Shira ta Jihar Bauchin an fara su ne tun daga ranar Asabar da daddare har zuwa assubahin Lahadi.

Mazauna garin sun ce maharar sun je da bindigogi da bama-bamai wadanda su ka jefa wa gine-ginen.

Akalla yaro daya ya halaka a sabilin hare-haren.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Bauchi, DSP Haruna Muhammad, ya tabbatar da faruwar hare-haren da kuma halaka yaron.

Karin bayani