Mutanen Rio de Janeiro sun fusata kan kisa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mutanen Rio de Janeiro na kone-kone bisa zargin 'yan sanda da kisan mutum biyu

Mazauna wani garin talakawa da ke kusa da babban birnin kasar Brazil wato Rio de Janeiro sun bankawa ababen hawa wuta, tare da toshe hanyoyin mota, domin nuna fushinsu da kisan wasu mutane biyu da suka yi arrangama da 'yan sanda.

Kafar yada labaran yankin ta rawaito cewa daya daga cikin mamatan ya rasa ransa ne sanadiyyar harbinsa da harsashin da 'yan sanda suka harba a lokacin da suke musayar wuta da wani da ake zargin mai safarar miyagun kwayoyi ne.

An dai harbi mutumin ne akan hanyar sa ta zuwa Cochi shi da iyalansa a ranar juma'a.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun ce kimanin mutane dubu biyu ne suka rasa rayukansa a Brazil cikin shekara guda, dalilin sakaci da tashin hankali kan hukuncin da 'yan sanda ke dauka a kasar.

Karin bayani