Chibok: Karin 'yan mata 7 sun kubuta

Hakkin mallakar hoto AFP

Gwamnatin Jihar Borno ta ce wasu karin 'yan mata bakwai daga cikin daliban da aka sace a makarantar sakandaren 'yan mata ta Chibok sun gudo daga hannun wadanda suka sace su.

Wata sanarwa daga gwamnatin jihar ta ce yanzu dalibai 52 ne suka kubuta yayin da ake cigaba da cigiyar wasu 77

A makon jiya ne wasu 'yan bindiga suka sace 'yan mata sama da dari a makarantar.

Gwamnatin Bornon ta yi alkawarin bada tukuicin naira miliyan 50 ga duk wanda ya bada bayanan da zasu kaiga kubutar da 'yan matan.