An gano gawarwaki 60 a jirgin Korea

Hakkin mallakar hoto Reuters

Adadin wadanda aka tabbatar sun mutu a wani hadarin jirgin ruwan Korea ta Kudu na karuwa, yayin da a karon farko, masu ninkaya suka iya kaiwa can cikin jirgin.

Kusan gawarwaki 60 ne aka gano kawo yanzu.

Kusan mutane 260, yawancin su yara kanana, har yanzu ake nema bayan jirgin ruwan ya kife.

Iyayen yaranda ke jirgin sun bayyana rashin jin dadin su akan irin jikinrin da suka ce anayi a aikin ceton.