An gano karin gawarwaki 13 a Korea ta kudu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Aikin ceto a Korea ta kudu na iya kaiwa makonni

Masu ninkaya da ke binciken jirgin ruwan Korea ta Kudu da ya nutse a ranar Larabar da ta wuce, sun yi nasarar samun gawawwaki goma sha hudu a cikin tarkacen jirgin.

Sun dai yi nasarar shiga cikin jirgin ne a karon farko ta tagoginsa.

A yanzu haka dai mutane arba'in da tara aka tabbatar da mutuwarsu, ya yin da ake neman fiye da mutane dari biyu da hamsin da yawancinsu kananan yara ne.

Wakilin BBC ya ce bayan shafe kwanaki ana fama da rashin kyawun yanayi, masu ninkayar Korea ta Kudu sun samu damar shiga cikin jirgin ta hanyar balle wunduna, gawawwakin na sanye ne da rigar kariya daga nutsewa cikin ruwa.

Masu shigar da kara sun ce a lokacin aukuwar lamarin sitiyarin jirgin na hannun wata jami'a da bata kware ba kuma ta na cikin ruwan da bata san shi sosai ba.

Karin bayani