An kara samun 'yan mata 7 sun tsira

Hakkin mallakar hoto NEMA
Image caption 'Yan mata 7 sun tsere daga hannun masu garkuwa da su

Gwamnatin Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ta ce wasu karin 'yan mata bakwai daga cikin daliban da aka yi awon gaba da su daga wata makarantar sakandare sun gudo daga hannun wadanda ke tsare da su.

Da tsakar daren ranar Litinin din da ta gabata ne dai wasu 'yan bindiga suka yi awon gaba da dalibai fiye da dari da ke rubuta jarrabawarsu ta karshe a makarantar sakandaren 'yan mata dake garin Chibok a Jihar ta Borno.

Gwamnan Jihar, Kashim Shettima, ya kuma bayyana cewa tun hawansa kujerar mulkin jihar bai taba tsintar kansa a mawuyacin hali kamar na makon nan guda ba.

Har yanzu ana ci gaba da kokarin ceto shauran da suke hannun 'yan bindigar.

Karin bayani