Win Tin na Burma ya mutu a shekaru 85

Hakkin mallakar hoto NLD
Image caption Win Tin ya mutu yana mai shakaru 85

Mutumin da ya fi kowa dadewa a gidan Wakafi a kasar Burma Win Tin ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru tamanin da biyar sanadiyar ciwon koda.

Mr Win ya kasance dan jaridar da ya taimakawa jami'iyyar National League for Democracy tare da shugaba Aung San Suu Kyi.

Ya dai shafe kusan shekaru goma sha tara a gidan kaso, bayan da aka same shi da laifin farfagandar kin jinin gwamnati.

An yi wa Mr Win ahuwa shekaru 6 da suka gabata, sai dai bai daina sanya rigarsa mai kalar sararin samaniya ta zaman gidan kaso ba a matsayin alamar rashin goyan bayan mulkin soja a kasar ta Burma.

Karin bayani