Chibok: Dalibai 'yan mata 230 aka sace

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Nigeria na sintiri a wasu yankunan arewa maso gabashin kasar.

Shugabar Makarantar 'Yan Mata da ke Chibok a Jihar Borno a arewacin Nigeria ta ce dalibai 230 ne aka sace a makon daya gabata.

Mrs Asabe Kwambura ta shaidawa BBC cewar bisa rijistar da suka bude a makarantar da iyaye suka bayyana cewar basu ga 'ya'yansu ba, shi ne aka samu wannan adadin.

A cewarta kawo yanzu 'yan mata 43 ne kawai suka kubuta daga hannun 'yan Boko Haram da ake zargin sun sace su.

Wadannan sabbin alkaluman na zuwa ne mako guda bayan da aka bada rahoton sace dalibai 'yan mata 129 a makarantar da ke Chibok.

Gwamnan Jihar Borno, Alhaji Kashim Shettima ya ziyarci makarantar a Chibok inda ya kwantarwa da iyaye hankali a kan cewar ana kokarin kubutar da 'ya'yansu.

Karin bayani