Shugabar Korea ta kudu ta nuna alhininta

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An sake gano wasu gawawaki a Korea ta kudu

Shugabar kasar Korea ta kudu, Park Geun-hye ta yi kakkausar suka ga jagoran jirgin da tawagarsa wadanda suka fice daga cikinsa a lokacin da ya nutse abinda ke kama da halayyar yin kisa.

Miss Park ta ce abinda suka yi ba za a lamunta ba.

A Korea ta kudun an sake gano karin wasu gawawwakin daga jirgin da ya kife makon da ya gabata yayin da masu ninkaya a ruwa suka sami damar kutsawa cikin jirgin sosai.

Yanzu adadin wadanda aka tabbatar sun rasu ya kai mutane sittin da hudu inda kusan dari biyu da arba'in har yanzu ba a gansu ba.

Karin bayani