Man United ta kori David Moyes

David Moyes Hakkin mallakar hoto v
Image caption 'Yan wasan Manchester United a filin kwallo

Kulob din Manchester United ya sallami mai horas da 'yan wasansa David Moyes, saboda rashin tabuka wani abin a zo a gani da kulob din ya yi a kakar wasanni ta bana.

Wata sanarwa da ta fito daga kulob din ta bayyana godiya ga David Moyes saboda jajircewarsa da kuma kwazonsa.

Moyes ya karbi ragamar horas da 'yan wasan kulob din na Manchester United ne a shekarar da ta gabata bayan mai horas da 'yan wasan kulob din na tsawon lokaci Sir Alex Ferguson ya yi ritaya.

Yayinda ya rage wasanni hudu kacal su kammala gasar Pirimiyar Ingila ta bana, Manchester United su ne na bakwai a jadawalin gasar.

Akwai kuma ratar maki ashirin da uku tsakaninsu da masu jagorancin teburin gasar wato kulob din Liverpool.

Manchester United ta kuma gaza samun gurbin zuwa gasar cin kofin zakarun nahiyar turai a karon farko cikin kusan shekaru ashirin.

Karin bayani