Korea ta Arewa ka iya gwajin Nukiliya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Korea ta arewa na shirin gwajin nukiliya

Wata majiyar Sojin Korea ta Kudu ta rawaito cewa a karo na hudu mai yiwuwa Korea ta Arewa na shirye-shiryen gwajin makamin Nukilyar ta.

Kakakin ma'aikatar tsaron Korea ta Kudu yace akwai alamun yawaitar shige da fice a garin Poon-gay-ree da ke arewa maso gabashin kasar, inda korea ta arewar ke gwajin makaman na ta.

Kakakin ya ci gaba da cewa watakila wannan gwaji ya na da alaka da ziyarar da shugaba Obama zai kai Korea ta Kudu a cikin makonnan.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce gwajin makamin nukiliyar da Korea ta Arewa ta yi a watan da ya gabata alama ce ta tsokanar fada, dan haka a yanzu ma ta bukaci Koriya ta Arewar ta bar wannan barazana.

Karin bayani