Atisayen tunkarar fashin teku a Nigeria

Wani jirgin yaki Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jiragen yaki na ruwa 22 na kasashen waje ne za su shiga atisayen

Kasashe 23 da suka hada da Amurka, Faransa da Jamus da wasu kasashen Afrika sun fara wani atisaye a Najeriya, domin tinkarar fashin teku.

A lokacin atisayen da zai dauki makonni uku, kasashen za su gwada wasu sabbin na'urorin tinkarar matsalar ta fashin teku.

Najeriya a 'yan shekarun baya-bayan nan, na fuskantar fashin teku da satar ma'aikatan jiragen ruwa da kuma yawaitar satar danyen mai a gabar tekunta.

Matsalar da ta bazu zuwa gabar tekun Guinea da kasashen da ke kewaye da shi, kamar su Kamaru da Benin da Gabon.