Shin akwai 'yan Boko Haram a Niger ne ?

Shugaban kasar Nijar Mahammadou Issoufou
Image caption Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar

Rahotanni na nuna cewa 'yan kungiyar Boko Haram a Najeriya na ci gaba da baza komar su don neman karin mayaka ko makamai da kuma shirya kai hare-hare a kasashe makota irinsu Nijar.

BBC ta samu tattaunawa da wasu 'yan kungiyar masu aikata laifuka a yankin kudu maso gabashin Nijar wadanda suka ce suna taimaka wa kungiyar Boko Haram, yayinda ita kuma take basu kudade.

Kasashe makotan Najeriya da suka hadar da Nijar, Kamaru da Chadi na tsoron cewa rikicin na Boko Haram ka iya watsuwa zuwa kasashensu, inda tuni dubban 'yan gudun hijira da ke gujewa rikicin suka kwarara.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla 'yan gudun hijirar Najeriya dubu hamsin ne suka nemi mafaka a Nijar kadai.

Wakilinmu Baro Arzika na cikin tawagar BBC ta da ziyarci yankin Diffa da ke yankin kudu maso gabashin Nijar da ke iyaka da Najeriya, ya kuma rawaito cewa akwai kungiya ta musamman da ke taimaka wa Boko Haram a can.

Matasa 'yan shekaru goma sha tara zuwa ashirin da uku ne ke cikin kungiyar, yawancinsu dalibai ne na makarantar sakandare.

Sun bayyana cewa rashin aikin yi na daya daga cikin dalilan da ya sa suke taimakawa kungiyar ta Boko Haram wadanda ke ba su kudade masu yawan gaske.