Amurka ta kalubalanci Rasha kan Crimea

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ziyarar Joe Biden a birnin Kiev

Mataimakin Shugaban Amurka, Joe Biden ya ce Amurka ba za ta taba amincewa da abin da ya bayyana, a matsayin haramtacciyar mamayar da Rasha ta yiwa Crimea ba.

Mr Biden na magana ne a Kiev a wata ziyarar da aka shirya don ya nuna goyon bayan gwamnatin Amurka ga gwamnatin rikon kwaryar Ukraine.

Biden yace "Babu wata kasar da take da 'yancin kwace fili haka kawai daga wata kasar, ba zamu taba amincewa da haramtaccen mamayen da Rasha ta yiwa Crimea ba, haka ma duniya ba za ta yi ba".

A cewarsa Ukraine, kasa daya ce wadda dole ne kuma ta ci gaba da zama daya.

Ya bukaci Rasha da ta yi aiki da wata yarjejeniyar da aka cimma a makon da ya wuce domin kawo karshen rikicin ta hanyar sa dakarun dake goyon bayan Rasha su bar gine-ginen gwamnatin da suka mamaye a gabashin Ukraine.

Karin bayani