Joe Biden na bayyana goyon baya ga Ukraine

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Amurka na goyon bayan Ukraine

Mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden, zai bayyana goyon bayan da Amurka ke bawa Ukraine karara a yau Talata a wani taro da za a yi a Kiev.

Ziyarar ta sa na zuwa ne kwana daya bayan Amurka da Rasha sun zargi juna da gazawa wajen kawo karshen zaman tankiya da ake a Ukraine.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya shaidawa takwaransa na Rasha Sergei Labrov cewa ya kamata Rasha ta fito karara ta yi kira ga 'yan awaren da ke dauke da makamai su fice daga gine-ginen gwamnati.

Shi ma Mr Labrov ya zargi gwamnatin Ukraine da ke samun goyon bayan Amurka da gazawa wajen hana magoya bayan Ukraine tada husuma.

Shi ma Kakakin Fadar White House Jay Carney zargin Rasha ya yi da cewa ta gaza wajen magance rikicin da ake yi a gabashin Ukraine.

Karin bayani