An samu tashin hankali a Brazil

Tayoyi da kananan motoci na cin wuta a Brazil Hakkin mallakar hoto GETTY
Image caption An ji karar tashin bindigogi akwai kuma tarin mutane da suka hallara a hanyar shiga garin

Wani mummunan tashin hankali ya barke a birnin Rio na Brazil, kasa da watanni biyu da ya rage kasar za ta karbi bakuncin gasar wasan kwallon kafa ta duniya.

Arangamar wadda aka yi tsakanin 'yan sanda da mazauna wani yanki na 'yan kama wuri zauna.

Hakan ya biyo bayan kisan wani mutum da iyalansa suka ce 'yan sanda ne suka yi ma dukan tsiya har lahira bayan sun kuskure shi da wani dillalin miyagun kwayoyi.

An toshe manyan hanyoyi na Copacabana lokacin da masu zanga-zanga daga wata unguwar ta talakawa, suka cinna wa kananan motoci da tayoyi wuta a kan hanyoyin.

Karin bayani