Manhajar bogi: Google na biyan kudade

Kamfanin Google Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tsarin shagon Google ya haramta ikirarin da ba na gaskiya ba

Kamfanin matambayi ba ya bata na Google, ya fara mayar wa masu mu'amala da shi kudadensu, bayan sun sayi manhajar da ke bayar da kariya daga cutar virus ta jabu.

Wadanda abin ya shafa dai sun sayi mahajar ne daga wani shagon kamfanin na intanet.

Manhajar ta zama mafi karbuwa, inda a kalla aka sauke kimanin 10,000 kafin a cire ta daga shagon.

Wani shafin intanet mai yada labarai, mai suna Android police ne ya gano rashin sahihancin manhajar.

Baya ga biyan mutanen da suka sayi manhajar cikakken kudadensu, Google ya kuma ba su wasu kudaden da za su sayi wani abu a shagon.

Shafin na Android police ya bayyana cewa manhajar ba ta kare komai, sai dai sauya yanayin hoto.

Bayan fitowar wannan labari na rashin sahihancin manhajar ne aka cire ta daga shagon.

Ikirari na karya

Manhajar bogin ta fara bayyana ne a ranar 28 ga watan Maris, kuma an cire ta a ranar 6 ga watan Aprilu.

Masu mu'amala da Google sun sayi manhajar kariya daga cutar virus din a kan $3.99.

Kamar yadda shafin na Google ya bayyana, "Manhajar ta yi karyar cewa da mutum ya latsa za ta ba da kariya daga kamuwa da cutar virus, amma a hakikanin gaskiya ba ta yi."

Kamfanin ya kuma kara da cewa, cikin kwanaki 14 masu zuwa duk wanda ya duba asusun ajiyarsa na banki, zai ga an dawo masa da kudadensa.

Sai dai wanda ya kirkiro manhajar fasahar, Jesse Carter a wata hira da jaridar Guardian, bayan an janye manhajar, ya bayyana cewa hakika an yi kuskure babba tun da ba a yi niyyar sakinta ba.