Kungiyoyin Fatah da Hamas sun hade

Image caption Falasdinawa sun yi murnar wannan hadewar

Kungiyoyin Falasdinawa masu hammaya da juna, Fatah da Hamas sun amince su kafa gwamnatin hadin kan kasa, bayan shekaru bakwai suna hammaya a kan batun iko da zirin Gaza.

Sun sanarda cewar za a kafa sabuwar gwamnati cikin makonni biyar masu zuwa sannan kuma a gudanar da zabukan kasa bayan karin watanni shida.

Hakan na zuwa ne bayan tattaunawa tsakanin Isra'ila da kungiyar Fatah ta Shugaba Abbas ta ci karo da matsala.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce Mr Abbas ya zabi yin sulhu da 'yan Hamas a maimakon Isra'ila.

Rahotanni sun ce jim kadan bayan sanar da yarjejeniyar, sai Isra'ila ta kadammar da hari a arewacin Gaza, lamarin da ya raunata mutane hudu.

Karin bayani