An dage taron Jonathan da Gwamnoni

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

An dage taron da aka shirya yi tsakanin Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan da gwamnonin kasar a kan batun kalubalen tsaro.

A ranar Laraba aka shirya yin taron amma kuma sai aka dage zuwa ranar Alhamis.

Kawo yanzu gwamnati ba ta bada cikakken bayani game da dalilan dage taron ba.

Tuni wasu gwamnonin kasar suka ce za su tsage gaskiya komai dacinta a wannan tattaunawar.

Gwamnan Jihar Adamawa, Murtala Nyako ya shaidawa BBC cewar ba za su bari a yi wani boye-boye ba a lokacin taron.

Nigeria na fuskantar tabarbarewar tsaro a 'yan watannin nan, inda galibin 'yan kasar ke kallon gwamnatin kasar ta gaza wajen kokarin magance matsalar.

Karin bayani