Wani dan majalisa zai kalubalanci Assad

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Bashar Al-Assad

Shugaban majalisar dokokin Syria ya ce wani dan majalisa ya yi rijista a matsayin mutum na farko da zai kalubalanci Shugaba Bashar Assad a zaben Shugaban kasa mai zuwa.

Maher Abdul -Hafiz Hajjar zai tsaya takarar zaben ranar uku ga watan Yunin da ake sa ran Shugaba Assad zai lashe.

Shugaba Assad na yin takara a karo na uku na wa'adin shekaru 7.

Kasashen yamma sun yi tir da shawarar gudanar da zabe a kasar duk da yakin basasar da kasar ke ciki na tsawon shekaru uku.

Karin bayani