Obama zai fara rangadi a yankin Asia

Shugaban Amurka Barack Obama na shirin tafiya Asia Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Amurka Barack Obama na shirin tafiya Asia

Shugaban Obama zai fara rangadi a yankin Asia, don cimma yarjejeniya da kasar Japan kan bude kasuwannin kayan da Amurka ke samarwa.

To amma a bisa dukkan alamu batun China ne zai mamaye abubuwan da zai tattauna a kansu.

Chinar na yunkurin karfafa ikirarinta na mallakar yankin tekun gabashin kasar mai cike da takaddama.

Sai dai Japan na bukatar samun tabbaci na goyon bayan soji daga Amurka a yayinda take kara fuskantar barazana daga China.

Dukkannin kasashen biyu dai na ikirarin mallakar yankin dake gabashin tekun China.

Har yanzu dai shugaba Obama na dari-dari da nuna goyon baya ga kasar Japan din babbar aminiyar Amurkar.