Barack Obama ya isa Japan

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Amurka da Japan suna dasawa

Shugaba Obama ya isa Japan a somin wata ziyarar yankin Asiya wadda kawayen Amurka ke neman tabbaci a takaddamar yankin kasashensu da China.

A cikin wata hira tare da wata jaridar Japan, Shugaba Obama ya ce Amurka za ta yi adawa da duk wani kokari na yin makarkashiya ga Shugabancin Japan a tsibirin Sekanku ko Diaoyu a gabashin tekun China.

Ma'aikatar harkokin waje ta China nan da nan ta nuna rashin yarda, tana mai cewar ya kamata Amurka ta rike alkawarinta na kin goyon bayan wani bangare a rikicin.

Shugaban Obama zai ci abincin dare tare da Pirayim Minista, Shinzo Abe sannan kuma suyi karin tattauna a ranar Alhamis.

Ana saran shugabannin biyu za su kuma tattauna a kan kokarin cimma yarjejeniyar cinikayya,kuma ana ganin samun ci gaba a hakan a matsayin wani muhimman abu a kokarin Amurka na sake gina tagomashinta a yankin.

Karin bayani