Fatakwal ta zama cibiyar litattafai ta duniya

UNESCO Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Manyan marubuta kamar shahararren marubucin nan na Nigeria da ya ci kyautar Novel, Wole Soyinka ya halarci bikin

Hukumar kula da ilimi da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya, UNESCO ta ayyana birnin Fatakwal na Nigeria, a matsayin cibiyar litattafai ta duniya ta 2014.

Wannan mataki wani bangare ne na bikin ranar Littattafai da hakkin mallakarsu ta Duniya.

Daya daga cikin muhimman abubuwan da ake sa ran gani a birnin na Fatakwal a tsawon shekarar shi ne, taruwar wasu marubuta 39 daga fadin nahiyar Afrika.

Marubutan za su tattauna a kan batutuwan da suka shafi adabi ta talifi a watan Oktoba.