Chibok:Kungiyoyin mata sun yi Allah wadai

Image caption Wasu daga cikin 'yan mata da suka kubuta

Kungiyoyin mata a Najeriya na cigaba da nuna bacin ransu, tun bayan da wasu maharan da ake zargin 'yan Boko Haram ne, suka sace wasu 'yan mata 230, daga wata makarantar sakandare a garin Chibok na jahar Borno.

Yayin da wasu 'yan matan kalilan suka samu suka kubuta, har yanzu akwai wasun fiye da dari da tamanin ba a san inda suke ba.

Wasu kungiyoyin mata a jahar Borno sun yi taron manema labarai a Maiduguri, inda suka yi kira ga maharan da su sako 'yan matan, sannan su shiga sasantawa da gwamnati.

Shugabar kungiyar Baobab, Farfesa Hauwa Abdu Biu ta yi Allah wadai da sace 'yan matan a Chibok da kuma wasu da aka sace kwanakin baya a Dikwa, inda ta ce hakan na kawo cikas ga ci gaba mata a jihar da kasar baki daya.

A halin yanzu dai iyayen 'yan matan da aka sace na ci gaba da zaman zullumi a kan makomar 'ya'yansu da aka sace kwanaki tara da suka wuce.

Karin bayani