Chibok: Dakarun Nigeria sun yi abin kunya

Image caption Wasu daga cikin 'yan matan da suka kubuta

Wasu daga cikin iyayen yaran da aka sace 'ya'yansu a Chibok da ke jihar Borno sun shaidawa BBC cewar gwamnatin kasar ta gaza wajen ceto 'ya'yansu daga wurin 'yan Boko Haram.

Kwanaki goma kenan da aka sace daliban 'yan mata a makarantarsu da ke Chibok, amma har yanzu dakarun Nigeria basu iya kubutar da su ba, abinda iyayen suka bayyana a matsayin abin kunya.

'Yan bindiga da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka dirar wa makarantar cikin dare inda suka sace dalibai 'yan mata 230.

Kawo yanzu bayanai sun nuna cewar 'yan mata kusan 50 sun kubuta a yayinda 'yan mata kusan 180 har yanzu su ke hannun 'yan Boko Haram din.

A cewar wasu iyayen, idan har gwamnati ba za ta iya ba, to ta nemi gudunmuwar wasu gwamnatocin kasashen waje.

'Dauki daga waje'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakaru na sintiri a cikin Maiduguri

Daya daga cikin iyayen wanda bayason a fadi sunansa, ya ce "Mun saido ga Allah, Allah ya yi mana jagora, hankalinmu a tashe yake, mun rasa yadda zamu yi".

Ya kara da cewar "Ina ganin cewar lamarin ya fi karfin jami'an tsaron Nigeria saboda haka su nemi agaji daga wasu kasashen".

Kungiyar Boko Haram wacce keda sansantinan a jihar Borno ta janyo mutuwar dubban mutane a Nigeria ta hanyar kisa da bindiga, dasa bam da kuma yankan rago.

Galibin al'ummar Nigeria na ganin cewar gwamnatin Shugaba Jonathan ta gaza wajen kawo karshen zubar da jani.

Ita kuwa gwamnatin cewa take tana iyaka kokarinta don murkushe ayyukan 'yan Boko Haram.

Karin bayani