Jonathan na tattaunawa da Gwamnoni

Image caption Shugaba Jonathan na shan suka game da tsaron Nigeria

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan na tattaunawar koli da ta shafi tsaro tare da wasu gwamnonin jihohin kasar, da shugabannin fannin tsaro da kuma malaman addinai.

Wakilin BBC a fadar Shugaban Nigeria ya ce kawo yanzu gwamnoni 25 sun halarci zaman tare da mataimakan gwamnoni tara.

Manyan hafsoshin tsaron kasar da Sufeto Janar na 'Yan Sanda da kuma manya jami'an tsaro duk suma suna cikin tattaunawar.

An gayyaci Sarkin Musulmi da Shugaba kungiyar Kiristoci-CAN duk don su bada tasu gudunmuwar a taron.

Wannan tattaunawar na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke fuskantar matsalolin tsaro musamman ayyukan 'yan Boko Haram.

Karin bayani