Mali na tuhumar Sanogo da laifin kisa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kyaftin Amado Sanogo

Masu shigar da kara a Mali sun tuhumi mutumin da ya jagoranci juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar a shekara ta 2012 da laifin hada baki don aikata kisa.

Kyaftin Amadou Sanogo, wanda yanzu haka yake zaman gidan yari bisa zargin sace mutane, ya jagoranci juyin mulkin ne da ya kai ga 'yan aware da masu fafutikar Islama suka kama yankin Arewacin Mali.

Jim kadan bayan kama Sanogo din a bara, an gano wani katon rami dauke da gawawaki fiye da 20, wadanda aka yi imanin cewa na wasu hafsoshin soja ne dake biyaya ga hambararren shugaban kasar, Amadou Toumani Toure.

Tun daga shekara ta 2012 zuwa yanzu kasar ta Mali na fuskantar matsalolin tsaro musamman a arewacinta.

Karin bayani