Boko Haram: Nigeria na bukatar taimako

Boko Haram Najeriya Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Boko Haram Najeriya

Wani babban jami'in Nijeriya ya ce kasar sa za ta yi marhabin da taimakon kasashen waje a yaakin da take yi da kungiyar Boko Haram.

Mataimaki na musamman ga Shugaban Nijeriyar Mr Doyin Okupe ya gaya ma BBC cewar irin yadda aka tura sojan Faransa suka jagoranci tsoma bakin soji a kasar Mali alama ce da ta nuna wannan taimako yana aiki.

Mr Okupe yace, ana kuma bukatar goyon baya daga kasashen yankin kasancewar 'yan Boko Haram din suna gudanar da harkokinsu ne daga kan iyakoki da suka hada kasar Nijer da Chadi da Kamaru ta bangaren arewaci da gabashi.

Sojojin Nijeriya dai sun gaza kwantar da wutar tashe-tashen hankulan da ake fama da su a yankin arewacin kasar.