Takunkumi ga bangarorin dake fada a Sudan ta Kudu

Sudan ta Kudu Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sudan ta Kudu

Wakilai a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na duba yiwuwar saka takunkumi ga bangarorin dake fada da juna a Sudan ta Kudu.

A wani sharhi da ta yi Jakadiyar Amurka Samantha Powell ta ce, lallai ne al'ummar duniya su dauki mataki a kan wadanda ke kai wa fararen hula hari da dagula harkokin siyasar kasar.

Tun farko jagoran kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya Herves Ladsous ya zargi bangarorin biyu da rashin amincewa ga shirin zaman tattaunawar sulhu.

A baya-bayan nan dai akwai alamun rikicin na Sudan ya kara rincabewa, yayinda ake ba da rahotannin kisan mutane masu dimbin yawa a rikicin kabilanci.

Tun cikin watan Disambar bara ne tashin hankalin ya barke a kasar.