Dakarun Ukraine sun nufi gabashin kasar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Ukraine na fafatawa da 'yan aware

Gwamnatin Ukraine ta ce sojojinta sun danna zuwa birnin Slavyansk na gabashin kasar inda 'yan aware da ke goyon bayan Rasha suke da karfi.

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Ukraine ta ce an lalata wasu wuraren binciken ababen hawa uku da kungiyoyin masu dauke da makamai ba bisa ka'ida ba, suka kafa.

Ma'aikatar ta kara da cewa an hallaka akalla mutane biyar da ta bayyana da cewa 'yan ta'adda ne.

Rahotanni na baya-bayan nan, sun ce wasu motoci masu sulke na sojan Ukraine, yanzu sun janye daga birnin, kuma wani wakilin BBC da ke wurin, ya ce kura ta lafa a tsakiyar birnin.

Har yanzu dai, masu fafutika da ke goyon bayan Rasha, suna cigaba da mamaye gine-ginen gwamnati a birane da dama na gabashin kasar ta Ukraine.

Karin bayani