An kashe mutane 260 da sace shanu 2,501 a Filato

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An dade ana fama da rikici a jihar Filato

Rundunar tsaro ta hadin gwiwa-STF a Jos da ke Jihar Filaton Nigeria ta ce an kashe mutane 260 tare da sace shanu 2,501 a cikin watanni shida a Jihar.

A cewar rundunar tsaron a cikin wannan lokacin da 'yan bindiga suka kadammar da hare-hare, an gano shanu 1,312 da aka sace da kuma makamai da alburusan 'yan bindigar da dama.

Kakakin STF din, Kyaftin Ikedichi Iweha ya tabbatarwa BBC wannan adadin a wata hira ta wayar tarho.

Galibin shannun an sace su ne a kananan hukumomin Mangu, Bokkos, Barkin Ladi, Shendam, Jos ta Kudu, Riyom, Langtang ta Arewa da kuma Langtang ta Kudu.

Rundunar tsaron ta ce tana aiki iyaka yinta domin tabbatar da tsaro rayuka da dokokin al'ummar jihar ta Filato.

A cewarta, ta samu nasarar damke wasu dillalan makamai wadanda ke baiwa masu satar shanu makamai.

Jihar Filato ta dade tana fama da rikici mai nasaba da addinni ko kabilanci kuma kawo yanzu an kasa gano bakin zaren warware matsalar.

Karin bayani