Harbe-harbe a wasu kauyukan Borno

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakarun Nigeria na sintiri a jihar Borno

Mazauna garin Chibok na jahar Borno, inda a makon jiya aka sace dalibai 'yan mata 230-sun ce sun kwashe daren jiya (Alhamis) suna jin karar fashewar manyan bama-bamai.

Suka ce sun yi ta jin karar har tsawon fiye da awoyi biyar a wasu kauyuka da ke yankin.

Hakan na faruwa ne yayin da ake cigaba da zaman zullumi dangane da 'yan mata 'yan makaranta da ake zaton 'yan Boko Haram ne suka sace su daga wata makarantarsu.

Babu tabbacin ko 'yan Boko Haram da ake zargi da satar 'yan matan ne suke kai hari a wani wurin, ko kuma sojojin Najeriyar ne ke kaddamar da farmaki.

Mahukuntan Najeriyar dai sun ce suna iya kokarinsu don ceto 'yan matan, wadanda ake tsammanin 'yan Boko Haram na tsare da su a dajin Sambisa da ke kusa da wurin.

Karin bayani