'Na ga 'yan matan Chibok da aka sace'

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kusan makonni biyu kenan da sace 'yan matan

A karon farko BBC ta samu shaida wacce ta ce ta yi ido biyu da wasu 'yan mata da ake zaton 'yan matan nan ne da aka sace a Chibok.

Shaidar wacce ta bukaci a boye sunanta saboda dalilai na tsaro, ta shaida wa BBC cewa ta ga 'yan matan ne tare da wasu 'yan bindigar da ake zargin 'yan kungiyar nan ne da ake kira Boko Haram a yankin karamar hukumar Gwoza dake jihar Borno.

Ta kuma gansu ne cikin motoci masu fenti irin na sojoji kimanin 11 da kuma babura.

Hakazalika bayanan da BBC ta samu na nuna cewa mayakan kungiyar kan shiga yankin, musamman kowace ranar Juma'a.

Bayanan sun kuma kara da cewa 'yan Boko Haram na gudanar da al'amura son ransu a yankin, saboda babu jami'an tsaro a can.

Babu dai wata majiya ta daban da ta tabbatar da ikirarin shaidar da BBC ta yi magana da ita, kuma kawo yanzu babu martanin jami'an tsaro game da wannan batu.