Nigeria: An dakatar da fim akan yakin Biafra

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wanda ya shirya fim din da kuma marubuciyar 'Half of a Yellow Sun'

Hukumar tace fina-finai ta gwamnatin Nijeriya ta dakatar da nuna wani fim mai suna, 'Half of a Yellow Sun' wanda aka yi shi akan yakin Biafra.

Dama dai an shirya za a soma fim din a gidajen sinima na Nijeriya ne daga ranar Juma'a.

Wata kakakin hukumar tace fina-finan ta fadawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, ba wai an haramta fim din ba ne, an dai dakatar da nuna shi a Nijeriya ne.

An shirya fim din ne akan littafin da Chimamanda Ngozi Adichie ta rubuta akan yakin Biafra da aka yi a tsakanin 1967 zuwa 1970.

Yayin yakin na basasar Nijeriya dai an kashe mutane fiye da miliyan guda.

Wanda ya shirya fim din, Biyi Bandele ya ce, shi har yanzu bai san dalilin da ya sa aka dakatar da fim din ba.