Chibok: Wajibi ne a ceto 'yan-mata

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Taron da Shugaban Najeriya ya yi da manyan jami'an tsaro, da gwamnonin jihohi ya yanke shawarar kubutar da 'yan-matan nan na Chibok.

Gwamnan Ekiti Mr. Kayode Fayemi ya ce batun da ya fi daukar hankali a taron shi ne na 'yan matan nan da aka sace, a wata makarantar sakandare dake garin Chibok a jihar Borno.

Mr. Fayemi ya ce hukumomin soji sun tabbatar da cewa suna duk abin da ya dace domin kubutar da 'yan matan.

Ministan tsaron Najeriya Janar Aliyu Gusau ya ce an tattauna dukkanin matsalolin tsaron da suka addabi kasar, kama daga yankin arewa-maso-gabas da satar shanu da satar mutane domin karbar kudin fansa da sauransu.

Taron ya kuma tattauna a kan wata takarda da ta jawo cece-kuce da gwamnan Jihar Adamawa ya aikewa takwarorinsa na jihohin arewa, wadda a ciki ya yi ikirarin cewa ana yi wa yankin arewacin kasar makarkashiya.